Kundin Kannywood

Adam A Zango an ji Jiki, ya ce ba zai kara sakin Aure ba

Fitaccen Jarumin Masana’antar Kannywood ƙarshe ya sha alwashi, gamida albishir mai daɗaɗa kunnai ga mai dakinshi da zata amarce dashi kwanan nan. Tuni Adam A Zango ya kammala shiri tsab domin angwancewa a karo na shidda cikin shekara 13. A katin gayyatar ɗamun auren da ya hauda kundinshi na wata kafar sada zumunta, Zango ya ce zai angwance da Sahibarshi mai suna Safiya Umar Chalawa, wadda aka fi kira da Suffy, a ranar Juma’a mai zuwa da misalin karfe 2:30 na rana. Za’a ɗarma auren ne a Masallacin fadar Sarkin Gwandu da ke garin Gwandu, a Jahar Kebbi.

Da yake nuna dokinshi a kan sabuwar amaryar da zai aura, Zango ya ce yana gayyatar kowa da kowa zuwa ɗamun aurenshi. Sannan ya kara da rubuta cewa zai kasance da sabuwar amaryar har abada. “Zan auri sahiba ta, Safiyya, kuma za ta kasance mata ta har abada Zan zamna tare da ita har abada,” a cewar sho.

Daga baya kuma jarumin ya ɗora wani faifan bidiyo na sabon gidansho da ake dab da kammalawa. A faifan bidiyon, ya rubuta, “Ina mai gabatar da sabon gidana ga amarya ta. Na kagu na gan ki a cikin gidan nan.”

Adam A. Zango Source: UGC Majiyar mu ta sanar da mu cewar Zango ya yi aure sau biyar a baya, ya samu ɗiya shidda; hudu maza, biyu mata, daga mata biyar da ya aura kafin su rabu. Amina ce matar Zango ta farko da ya aura a shekarar 2006. Ita ce uwar yaron shi na farko, Haidar, wanda yanzu haka ya cika shekara 12 da haihuwa(Kuma shi muke zaton zai gadeshi don tuni ya fara wakokin Hausa hiphop). Majiyar mu ta ce ba ta san abunda ya raba auren Zango da Amina ba. Zango ya kara auren wata mata mai suna A’isha, ‘yar asalin Shika ta karamar hukumar Zaria a Jahar Kaduna. Ta haifa ma shi diya maza ukku. Jarumin ya auri matar shi ta ukku mai suna Maryam daga Jahar Nasarawa.

Daga bisani ya auri wata jarumar Kannywood mai suna Maryam AB Yola a Lugbe, Abuja a shekarar 2013. Sun bayyana tare a cikin wani faifan shirin Hausa mai suna ‘Nas’ A shekarar 2015, Zango ya auri Ummul Kulsum daga Ngaoundere a Jamhoriyar Kamaru. An yi auren a sirrance. Ummul Kulsum ce ta fara haifa ma Zango diya macce, wadda ya sanya ma suna Murjanatu. Safiyya ko kuma Suffy kamar yanda ake kiranta, ita ce za ta kasance matar Zango ta shidda da ya aura. Majiyar mu ta ce Zango ya saki dukkan matan biyar da ya aura a baya, sai dai har yanzu ba ta san dalilin rabuwar shi da matan da ya ke aura ba. Allah ya tabbatarda alheri.

Madogara: Legit Hausa

DanZubair

Multilingual Blogger, Website and Graphic Designer, Gobir Enthusiast, GTE at WordPress Hausa. I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder- Operator at Bago Technologies. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published.