Labaran yau da kullum

Aliko Dangote zai zuba Zunzurutun Kudi ga harkar Kiwo da Noma

A hirar ɗaya daga daraktocin kamfanin Dangote ran Talata, Edwin Devakumar, yace rashin kuɗaɗen shiga shi yassa kamfanin zuba jari a harkar noman gargajiya dan samarda kayan abunci ga mutane Nijeriya fiye da miliyan dari da tamanin (180).

A shirin Shugaba Muhammadu Buhari na rage dogaro 100% ga man fetur, Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya ɗauki anniyar sa hannu jari a harkar noma. A shirin nashi, Attajirin na Afrika na shirin sa kudi zunzurutu har dala miliyan ukku da ɗigo takwas ($3.8) a noman rakke da shinkafa da dala miliyan dari takwas ($800 milion) ga madara.

Dangote na shirin noman filaye da kimanin faɗinsu zai kai eka dari ukku da tamanin (380) dan noman karan rakke da ƙarin eka dubu dari biyu (200,000) dan noman shinkafa, ta bakin Devakumar.

Injinukkan tatar sukari biyar (5) da na sarrafa shinkafa goma (10) na bisa hanyarsu daga kasar Switzerland zuwa Arewacin Nijeriya, yacce.

Ta bakin kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) estimates, yan Nijeriya nada buƙatar litocin madara biliyan daya da ɗigo biyar (1.5) kowace shekara.

Kamfanin zai kyayaci shanu dubu hamsin cib-cib dan samarda litocin madara bila adadin.

DanZubair

Multilingual Blogger, Website and Graphic Designer, Gobir Enthusiast, GTE at WordPress Hausa. I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder- Operator at Bago Technologies. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published.