Labaran yau da kullum

An bayyana Sunayen Mutanenda Coronavirus ta kashe a Nijeriya

Tun bayan ɓullar cutar Coronavirus ko COVID-19 mutane ke ta ƙwanƙwanton yarda da labarin yaɗuwarta a Nijeriya da sauran ƙasashen nahiyar Afrika, ganin cewa ba’a fadin sunayen waɗanda cutar ke kashewa ko kamawa sai dai kullum aji adadinsu yana ta ƙaruwa. To yanzu mun samu labari daga wata ƙungiyar ƴan Nijeriya dake zama ƙasashen waje da ta bayyana sunayen mutanenta da sun ka mutu sanadin cutar. Mutanen su wajen goma sha-ukku (13) ne; akwai ƴan Kudu da ƴan Arewa a ciki. Muna musu addu’ar Allah yasa kwanciya hutu, ya kuma kawo sauƙin cutar a illahirin faɗin duniya. Ameen.

Shugaban kungiyar yan Nijeriyar mazamna ƙasashen ƙetare wato Nigerians in Diaspora (NIDCOM) ya zayyano sunayen ƴan Nijeriya da cutar mashaƙo ta kashe a ƙasashen waje. Abike Dabiri-Erewa ya bayyana hakan ne ta faifan bidiyo a kundinshi na kafar Twitter inda yayyi addu’a garesu kamar haka:

May the souls of our brothers and sisters in Diaspora, who lost their lives to Covid-19, RIP. May the lord heal the world.

Ga adadin sunanyen wadanda cutar ta kashe ƴan asalin Nijeriya:

 1. Alfa Sa’adu (United Kingdom)
 2. Carol Jamabo (United Kingdom)
 3. Bode Ajanlekoko (United Kingdom)
 4. Bode Abayomi, SAN (United Kingdom)
 5. Adeola Onasanya (United Kingdom)
 6. Ugochukwu Erondu (United Kingdom)
  7.Chidinma Olajide (United Kingdom)
 7. Bassey Offiong (USA)
 8. Caleb Anya (USA)
 9. Mmaete Greg (USA)
 10. Akeem Adagun (USA)
 11. Laila Abubakar Ali (USA)
 12. Patricia Imobhio (USA)

DanZubair

Multilingual Blogger, Website and Graphic Designer, Gobir Enthusiast, GTE at WordPress Hausa. I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder- Operator at Bago Technologies. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published.