Gargajiya da Tabi'u

Gatan-gatan ku- Gatanar Kura Da Dan Tumkiya

Wannan gatanar Kura ce da Dan Tumkiya. Gatanan, gatananku. Ta je ta dawo. Wata rana kura tana yawo sai ta hangi dan Tumkiya yana shan ruwa a gefen hanya sai nan-da-nan tayi tunanin dubarar da zata yi ta kasheshi, nan take sai ta gusa inda yake shan ruwa kamar itama zata sha sai tace ma shi, “Ta yaya zaka bata ruwan da nake sha” jikinshi na rawa yace ranki shi dade ta yaya zanyi haka ai ma kuma ruwan ta wurinki su ka fara biyowa sannan su iso gareni. Sai kura ta sake ce ma shi, “Aima shekarar data wuce kaine ka la’anci uwata” Sai yace aini shekarar data wuce bama a haifeni ni ba. Da taji haka sai tace to lalle zakayi ta ‘yan dubarunka amman yau sai na lakume ka. Kunkur kan kusu.
DARASI
Wannan yana nuna muna idan har mutum yayi niyyar kulla sharri a rayuwarshi to komi girman hujjoji da gaskiyar da za’a nuna ma shi ba zai hana shi aikatawa ba. Allah yasa mu kasance masu aikata alheri Amin.

Hassan Haruna Gobir

Chief editor and publisher at HausaToday. My main interest were on Everyday News, Culture and Traditions and History Corner.

Leave a Reply

Your email address will not be published.