Gidan JarumaiKundin Kannywood

Kannywood: Fati Bararoji na-shirin dawowa Harkar Kannywood (Photos)

Tsohuwar Jarumar Kannywood cewa da Fatima Baffa, wadda kun ka fi sani da Fati Bararoji, mai kimanin shekarun arba’in (40) da haihuwa ta ɗora wasu ƙayatattun kamannai na ta waɗanda ke nuna alamun za ta dawo Kannywood bayan ta shafe shekaru da dama ba ta masana’antar tun bayan auren ta a Birnin Lagos.

Mutane sun bar ganin ta bayan ta yi auren farin inda bayan ya mutu ta tsunduma harkar kasuwancin da ta ke kawo yanzu. GobirMob na-ma ta fatan alheri.

Mai yiwuwa za ta bi sahun su Fati Muhammed, Masurah Isa, Sa’adiya Gyale dss ne waɗanda ke aiki a katafariyar masana’antar amman ba su bayyana a matsayin jarumai kamar da.

An haifi Fati Bararoji a ranar 24 ga watan Disamba a Jahar Maradi, Jamhoriyar Niger.

Ga Ƙayatattun Kamannin ku kalla
Our Telegram Channel

Source
Hausaloaded.com

DanZubair

Multilingual Blogger, Website and Graphic Designer, Gobir Enthusiast, GTE at WordPress Hausa. I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder- Operator at Bago Technologies. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published.