Labaran yau da kullum

Senator Gobir ya bada Kyautar Kekunan ɗumki ga waɗanda Gobara ta shafa a Wurno

Ta bakin na hannun daman Senator Dr. Ibrahim Abdullahi Gobir mai waƙiltar yankin Sokoto-ta-gabas, Naziru Emir Gobir ya bada sanarwar cewa Maigidanshi ya hannata kyautar kekunan ɗumki ƙwara guda goma (10) ga Maji Kiran Sarkin Sudan dan jajantama Ƙungiyar Maɗumka a Wurno da bala’in gobara ya samesu kwanakkin baya a kasuwarsu dake cikin garin.

Sardaunan Gobir ya bada kyautar ne yayinda ya kai ziyarar gani da ido ta jajantawa bisaga bala’in da sun ka samu na asarar kekunansu na aiki da sauran kayan aikin ɗumki. Allah shi tsare shi ƙara kiyaye gaba. Ameen.

Ga wasu hotunan kekunan nan ƙasa:

DanZubair

Multilingual Blogger, Website and Graphic Designer, Gobir Enthusiast, GTE at WordPress Hausa. I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder- Operator at Bago Technologies. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published.