Labaran yau da kullum

Shin alaƙar da ke tsakanin Gwamna Tambuwal da ɗan wasan Super Eagles Abdullahi Shehu siyasa ce ko karramawa?

Kusan rabin jama’ar dake duniya nada sha’awar kwallon kafa wanda hakan yassa kwallo keda matukar farin jini ga al’umar kowace nahiya a fadin duniya wanda ma ko yawancin mutanen dake da abun yi sukan ji suna sha’awar kwallon kafa saboda yadda take jawo ma mutum suna da kuma farin jini a idon al’umma.
Wanda hakan yassa ana kammala wasan cin kofin duniya da ya gudana a kasar Russia Maigirma Gwamnan Jahar Sokoto Hon Aminu Waziri Tambuwal ya karrama dan wasan Sokoto tilo daya taba wakiltar Nijeriya a irin wannan gagarumar gasa ta kofin duniya inda har ya bashi gida
sai dai kuma a kwanannan wani al’amari da yawancin al’umma suke suka shine yadda Gwamnatin Jaha ta shirya wata gasa tsakanin kananan hukomomi 23 inda aka raba ma kowace karamar hukuma kayan sawa dauke da hoton Abdullahi Shehu da kuma gwamna Tambuwal da kuma wani rubutu mai bayanin Mutawalle 2019 wanda yawancin mutane ke cewa “Siyasa ce” ba wai jan hakalin matasa ba ganin anyi hakanne lokacin da zabe ke karatowa sai.

Hassan Haruna Gobir

Chief editor and publisher at HausaToday. My main interest were on Everyday News, Culture and Traditions and History Corner.

Leave a Reply

Your email address will not be published.