Labaran yau da kullum

Wani Sarki ya bada shawarwari yanda za’a shawo kan Matsalolin Arewa cikin gaggawa

Maimartaba Sarkin Gwandu ya koka kan yanda matsalolin Arewa musamman Zamfara, Kaduna da Katsina dss sunka ki ci sunka ki cinyewa duk da matakan da ake ta dauka,inda jiya ma yan bindiga sunka zo har cikin gari sunka yi garkuwa da surukin dogarin Shugaban Kasa, a Masarautar Daura. Maimartaba Alh Haruna Jokolo ya nuna bacin rai cewa a cikin Shugabancin Muhammadu Buhari ake ta wanda ta’asar kuma ya kasa cewa komi saboda na tareda shi sun mai asiri, sun hadashi da muyagun bokaye sun darme mai baki, sun hanashi gani, sun dade mai kunnuwa kar ya kula da Matsalolin Arewa balle yayi maganar shawo kansu. Yace dama ba kishin Arewa bane gabansu, burinsu shine su tara kudi, su tara dukiyarda ba mai irinta.

Sarkin gargajiyar yayi wannan maganar ne a wata hira da yayi wata jarida inda kara da bada shawarwarin kwato Shugaban daga tarkon da na taredashi sunka mai yace, “Addu’a da yan Nijeriya sunka yi ma Shugaba Buhari lokacin baida lafiya har yanzu ma ita zasu kara mai dan shawo kan matsalolin tsaro a Arewacin Nijeriya da ma kasa baki daya.”

Yayi kira ga Uwargidan Shugaban kasa, Mrs Aisha Buhari cewa ta dauki nauyin malamai su je Saudiya su ma Buhari addu’a Allah ya kwance asirin da aka mai. Talakawa, Sarakunan Gargajiya, Malaman kasa su ma suyi tasu addu’ar.

Karshe yayu kira ga na tareda Shugaban kasa, cewa su bar karkatarda shi.

DanZubair

Multilingual Blogger, Website and Graphic Designer, Gobir Enthusiast, GTE at WordPress Hausa. I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder- Operator at Bago Technologies. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published.