Labaran yau da kullum

Yanda wani Aboki ya kashe Dogarin Sarkin Saudiyya

Gidan Talabijin ɗin Ƙasar Saudiyya ya tabbatar muna da kashi da an ka yi ma wani babban mutum watau Babban Dogarin Sarki Salman Maj. Gen Abdulaziz Al-fagham wanda sun ka ce an halbe shi har lahira, kisan cin amana. Maj. Al-fagham dai ya gamu da mutuwar shi ne a lokacin da ya kai ma abokin shi Faisal Bin Abdulaziz al-sabti ziyara a Birnin Jedda amman kuma sai ga wani abokin shi da a ke kira da Mamdou Bin Mishal Al-ali ya zo wurin inda ba da jimawa ba an ka ji shi da General Al-fagham sun fara gardama inda nan take an ka ga Al-ali ya koma gida ya ɗauko bindiga nan take ya buɗe ma Mai. ɗin wuta tareda shi da wasu mutane biyu da ke wurin da kuma maigidan Turki Al-sabti.

Ƴan Sanda dai sun yi ƙoƙarin kawo ɗauki amman nan take su ma Al-ali ya bude ma su wuta inda sun ka yi nasarar halaka shi lokacin da sun ka maida wuta. An dai yi kokarin kai su Al-Fagham assibiti amman ba da jimawa ba Allah ya karɓi rayuwar Maj. Al-fagham amman sauran mutane su na da sauran kwana gaba inda yanzu likitoci na ba su kulawa Ƴa Sanda kuma su na cigaba da bincike.

Mu ma mun ce Allah ya jikan shi. Ya kuma tsare gaba.

Hassan Haruna Gobir

Chief editor and publisher at HausaToday. My main interest were on Everyday News, Culture and Traditions and History Corner.

Leave a Reply

Your email address will not be published.