Kundin Kannywood

Yau Sani Danja da Mansurah ke Bikin Murnar cika Shekaru goma sha-biyu 12 da Aure, ya ratata Kalaman Soyayya

Sani Musa Danja fitaccen jarumin nan wanda yake haska akwatunan kallonku, Mawakin Hausa hiphop da nanaye, Marayi, dan wasan kwaikwayo na gida Kannywood da na harshen Ingilishi Nollywood yau ya cika shekaru goma sha-biyu (12) cib-cib da aure da shi da uwargidanshi Mansurah Isah, auren da kawo yanzu yake shan yabo da kirari daga masharhanta dabam-dabam, saboda cewa an ginashi ne bisa tafarkin soyayya da shakuwa da juna.

Sani ya dora wasu hotuna guda biyu inda yake tareda Matarshi Mansurah. Ya sakaya hotunan da kalami da harshen Ingilishi in an fassara ta ke nufin Yau rana murna ta sake zagayowa ga iyalin gidan Danja. Muna gode ma albarkar da Allah. Allah ya cigaba da tsare mu duka. Ameen.

Ga ainahin kalaman:

Its another anniversary for the Danjas family. Thanking Allah for all the blessings. May Allah continue to guide us. Ameen

Sani Danja da Mansura Isah sunyi aure ne rana mai kama ta yau 14 ga watan Yuli a shekarar 2007. Allah ya albarkacesu da haihuwar diya guda hudu, macce guda daya (1) Kadijatul Iman da maza guda ukku (3) Ahmad da sauran kannanshi. Allah shi sa albarka.

DanZubair

Multilingual Blogger, Website and Graphic Designer, Gobir Enthusiast, GTE at WordPress Hausa. I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder- Operator at Bago Technologies. My hobbies are reading, travelling and discovering.

Leave a Reply

Your email address will not be published.